Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da naɗin Shamseldeen Babatunde Ogunjimi a matsayin mukaddashin Akanta Janar na Ƙasa.
Naɗin nasa zai fara aiki nan take bayan ritayar Akanta Janar mai barin gado, Dakta Oluwatoyin Sakirat Madein.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a cikin wata takarda da ya fitar a ranar Talata.
Mista Ogunjimi babban darakta ne a Ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF), yana da gogewa mai yawa a fannin sarrafa kuɗi, inda ya kwashe fiye da shekaru 30 yana aiki a ma’aikatun gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu. Ya rike muƙamai masu muhimmanci, ciki har da Daraktan Kuɗi a OAGF da Daraktan Kuɗi a Asusun Ma’aikatar Harkokin Waje.
Shugaba Tinubu ya jinjina wa Dakta Madein bisa sadaukar da ta nuna a lokacin aikinta. Dakta Madein za ta yi ritaya daga aikin gwamnati bayan cika shekarun ritaya a ranar 7 ga watan Maris din 2025.
Shugaba Tinubu ya naɗa mukaddashin akanta janar na Ƙasa