Ma’aikatar Matasa da Ci gaban Wasanni ta Jihar Taraba ta sanar da haɗin gwiwa da Kwalejin Wasanni ta Serbia.
Wannan haɗin gwiwa zai kawo horo da shaidar ƙwarewa ga masu horas da wasanni, likitoci, da masu kula da lafiyar ‘yan wasa a shekarar 2025.
Joshua Joseph, Kwamishinan Matasa da Ci gaban Wasanni na jihar, ya kuma bayyana cewa akwai wata sabuwar haɗin gwiwa da Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Serbia.
Wannan haɗin zai ba da damar samun shaidar ƙwarewa ta UEFA A, B, da C ga masu horas da ‘yan ƙwallo a Jihar Taraba.
“Da godiya ga Allah Madaukakin Sarki da kuma godiya ta musamman ga His Excellency, Dr. Agbu Kefas, Gwamnan Jihar Taraba, saboda goyon bayansa da jajircewarsa wajen tallafawa matasa.
“Muna farin cikin sanar da wannan haɗin gwiwa. Muna kuma ba da shawara ga dukkanin ’yan jihar Taraba da ke sha’awar samun horo da shaidar ƙwarewa a fannin wasanni ko sauran bangarorin motsa jiki, su gabatar da takardun CV da wasikar sha’awa ga ofishin Kwamishinan Matasa da Ci gaban Wasanni, ”in ji Joseph a cikin sanarwa.
Jihar Taraba ta kulla hadin gwiwa da kwalejin wasanni ta Serbia