SHARE

An rufe filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja na wani dan lokaci sakamakon sauka daga kan Titina rashin jirgi da jirgin Allied Air yayi.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya samu fashewar taya ne bayan da ya sauka a filin jirgin saman a ranar Laraba.

Rahotannin sun tabbatar da jirgin ya makale a kusa da titin tashin jirgin lamarin da ya sa aka rufe filin jirgin har sai lokacin da za a kwashe jirgin.

Kawo yanzu dai an tabbatar da babu wani fasinja da yaji rauni sanadiyar fashewar tayar. Filin jirgin ya cika da fasinjoji sanadiyar dakatar da tashin jiragen saman baki daya.

Hukumomi na cigaba da kokarin aikin gyara hanyar tashin jirgin da abin ya shafa.

Shehu Sani criticizes Emir Sanusi’s advice on domestic violence

NO COMMENTS