SHARE

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya jaddada cewa Najeriya tana kan hanyar samun manyan sauye-sauyen tattalin arziki sakamakon tsarin shugaban kasa na ‘Renewed Hope Agenda.

Ya ce za a samu habakar tattalin arziki, gina rayuwar yan kasa da samar da ababen more rayuwa, ƙirƙire-ƙirƙire, gasa, da ci gaba da zai amfanar da kowa.

Ministan ya bayyana cewa shirin sauye-sauyen kudirorin haraji da Shugaban Ƙasa ya gabatar zai sauƙaƙa tsarin haraji na Najeriya tare da rage nauyin haraji da marasa karfi a kasar ke biya.

An gabatar da dokoki guda huɗu da suka shafi sauye-sauyen haraji a gaban Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Amma akwai masu adawa da dokokin, musamman daga yankin Arewa, inda ake nuna damuwa kan wasu sassa.

Amma Shugaban Ƙasa ya umarci Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, da ya gana da ƙungiyoyin da ke adawa da kudrirorin domin magance duk wata matsala da su ke da ita.

Yayin jawabi a taron shekara-shekara na Kungiyar Kasa da Kasa ta ‘Yan Jarida (International Press Institute), Ministan yace: “Babban abin da aka fi maimaitawa a cikin wannan sauyi shi ne gabatar da sabbin rangwamen haraji da za su amfanar da rukunin mutanen Najeriya daban-daban da kuma kamfanoni.”

Tattalin arzikin Najeriya zai samu gagarumin ci gaba – Idris

NO COMMENTS