A kalla mutum 33,789 ne suka amfana da kungiyar ActionAid Nigeria ta hanyar wani shiri na musamman da aka gudanar tare da haɗin gwiwar Global Peace Development (GPD) a Jihar Kano da Kaduna.
Wannan na kunshe ne cikin bayanin bayan taron kammala shirin, da kuma taron bayyana sakamakon shirin a Kaduna.
Shirin na SARVE III na da nufin yaki da tsattsauran ra’ayi ta hanyar inganta haɗin kai cikin al’umma, karfafa su, da samar da damamamki ta fuskar tattalin arziki.
A cewar ActionAid, mata 23,004 da maza 10,785 suka amfana daga shirin.
Shirin ya kuma ƙarfafa juriya ta hanyar horas da mutane 606, ciki har da matasa maza 175 da mata 209, da kuma mata 222, tare da ba su ƙwarewa kan sana’o’i daban daban.
.
ActionAid Za ta tallafawa mazauna Kano da Kaduna fiye da 33,000