in

Juventus ta doke Man City

Manchester City ta kara dulmiya cikin matsala a ranar Laraba bayan da suka sha kashi 2-0 a hannun Juventus a gasar Champions League.

Kwallaye biyu da aka ci bayan hutun rabin lokaci daga Dusan Vlahovic da Weston McKennie sun tabbatar da nasarar Juve, wanda hakan ya jefa kungiyar Pep Guardiola cikin matsanancin hali, inda suke fuskantar hadarin ficewa daga zagaye na gaba

City, wadanda suka kasance zakarun Ingila, suna matsayi na 22 a gasar zakarun Turai, bayan sun tattara maki takwas kacal daga wasanni shida na sabon tsarin gasar.

Wannan na nufin City suna da maki daya kawai sama da na kungiyoyi 12 na karshe wadanda ke iya faduwa daga gasar, tare da wasanni biyu masu wahala da suka rage da Paris Saint-Germain da Club Brugge, matsayin da ba a zatarwa kungiyar ba tun farkon kakar wasan.

Sai dai kuma City sun rikice cikin kasa da makonni shida, suna nesa da sahun gaba a gasar Premier League da Champions League, sakamakon nasara daya tilo da suka samu akan Nottingham Forest tun karshen watan Oktoba.

Juventus ta doke Man City

NPFL: Remo Stars coach wants derby spoils against Ikorodu City

Majalisa za ta binciki ayyukan kwastam