Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shaidawa shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier cewa manufofin tattalin arziki da gwamnatinsa ta fara aiwatarwa na yin tasiri kuma Najeriya a shirye take ta kulla huldar kasuwanci da kasar Jamus.
Ya yi wannan jawabi ne a jiya a wani taron manema labarai na hadin gwiwa tsakaninsa da shugaban kasar Jamus da ya kawo ziyarar aiki Najeriya.
Shugaban ya ce tattaunawar da sukayi da shugaba Jamus tayi matukar tasirin
“‘yan kasuwarmu da masu tsara manufofinmu sun damu sosai don yin kasuwanci da Jamus saboda haka Ina ba ku tabbacin cewa kofofin kasuwancinmu a buɗe suke kuma gyare-gyaren manufofi da muka kawo suna aiki sosai wajen samar da cigaba.”
A nasa bangaren, shugaban na Jamus ya yabawa Tinubu kan yadda yake samar da zaman lafiya a tsakanin kasashen ECOWAS, inda ya ce a matsayinta na mamba a Tarayyar Turai, Jamus ta fahimci mahimmancin hadin kan yankin.
Ya ce Najeriya ita ce babbar abokiyar huldar kasuwanci ta biyu a kasar Jamus a yankin kudu da hamadar Sahara kuma shi ya sa yake farin cikin ganin an inganta huldar zuba jari a tsakanin kasashen biyu.
Sabbun manufofi tattalin arziki da muka bijiro dasu sunyi tasirin daya kamata – Tinubu