Gwamnatin Tarayya ta ce jihohi da dama da kuma Birnin Tarayya Abuja za su bi sahun kaddamar da sabon mafi karancin albashin daga Janairun 2025.
Ministan kwadago, Muhammad Maigari Dingyadi ne ya bayyana hakan a shalkwatar ma’aikatar a Abuja, lokacin da ya karbi tawagar kungiyar manyan Ma’aikatan gwamnati (ASCN), a ranar Alhamis.
Ya yi kira ga ma’aikatan da su kara hakuri, yana mai cewa ma’aikatar ba ta da kididdgar jihohin da suka aiwatar da dokar ba ko wadanda ba suyi ba.
A cewarsa, bisa ga bayanan da ma’aikatan suka bayar, jihohi hudu zuwa biyar basu bifara aiki da sabuwar dokar albashin ba, yayin da wasu kuma sun bi ta a wani mataki.
Ministan ya ce: “Abuja ta ce za ta fara biyan sabon albashin a watan gobe. Amma reshen birnin na kungiyar yana cewa sai a aiwatar da shi nan take. Wanda a cewarsa hakan bai dace ba.
Ya ce ma’aikatar ta lura da dukkan batutuwan da aka kawo.
Gwamnati za ta fara biyan ma’aikatan FCT mafi karancin albashi a Janairu, 2025