in

Za mu cigaba da rusau – Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya kare matakin sa na rusa gine-ginen da ake zargin an gina su a kan filayen gwamnati a Abuja, duk da suka da ya sha daga mazauna da masu gidajen.

Politics Nigeria ta ruwaito cewa rushe-rushen da Wike ke yi sun jawo cece-kuce, inda mutane da dama suka rasa gidajensu.

Wani kamfanin gine-gine, Paullosa Nigeria Limited, kwanan nan ta nuna damuwa kan sanarwar rusau da Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya (FCDA) ta fitar don rusa gidajensu a unguwar Lifecamp a Abuja.

Sai dai, Wike a ranar Alhamis ya nace cewa gine-ginen da ake rusawa an gina su ne ba bisa ka’ida ba a kan filayen gwamnati kuma suna kawo barazanar tsaro.

Ya sha alwashin cigaba da rushe-rushen, yana mai cewa: “Ko sama ta rushe.”

Ministan ya kuma mayar da martani kan zarge-zargen batanci da ake masa, inda ya ce ba zai bari tsoratarwa ko barazanar kowa ta hana shi yin aikinsa ba.

“Abin da ba daidai ba ne, ba zai taba zama daidai ba; babu wani irin batanci da zai hana mu aiki,” in ji shi.

“Ba za mu kyale wanda ya ke tunanin zai kwace filin gwamnati ba tare da izini ba. Ba za mu kalli fuskar kowa ba, ko da kuwa kai mai fafutuka ne ko kuma shahararren dan jarida.”

Wike ya gargadi mutane da har yanzu ke bin bashin kudaden haya na filaye a FCT da su biya, ko kuma su fuskanci kwace filayensu.

Ya jaddada cewa samar da tsaro shi ne babban aikin kowace gwamnati.

Za mu cigaba da rusau – Wike

‘Blackmail can’t stop us’ – Wike vows to end land grabbing in Abuja

Reps to probe alleged mismanagement of $232m loan under Buhari