An samu gwamnonin Najeriya da dama sun nuna goyon bayan samar da ƴan sandan jihohi.
An fadi haka ne a taron Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranta a ranar Alhamis.
Jihohi 35 sun gabatar da matsayarsu, inda yawancin gwamnonin suka nuna goyon bayan kafa ƴan sandan jihohi.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, da ya zanta da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa ya tabbatar da haka, amma ya ce sai a taron NEC na gaba da za a yi a watan Janairu 2025, za a ɗauki matsaya a kan lamarin.
A tuna cewa, a wani taro da aka gudanar a watan Nuwamba, jihohin Kwara, Kebbi da Adamawa sun bayyana ba su gabatar da matsayarsu kan batun kafa ƴan sandan jihohi ba.
“Yau, ɗaya daga cikin batutuwan da muka tattauna a taron NEC shine kafa ƴan sandan jihohi.”
“Yau, kusan jihohi 35 sun gabatar da matsayarsu kan kafa ƴan sandan jihohi a Najeriya. Kuma zan iya cewa, bisa bayanan da muke da su, kusan dukkan jihohin suna goyon bayan kafa ƴan sandan jihohi.”
Gwamnoni sun goyi bayan kafa ƴan sandan jihohi