SHARE

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta bada tallafin kayan abinci ga dubban yan gudun hijira da wanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa a jihar Zamfara.

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ne ya jagoranci bada tallafin a Gusau babban birnin jihar.

Gwamnan ya ce raba kayan wani bangare ne na ragewa al’ummar da abin ya shafa radadi yayin da gwamnati ke cigaba da kokarin kawo karshen wadannan matsaloli.

Da yake jawabi a madadain shugabar hukumar NEMA ta kasa Hajiya Zubaida jami’i mai kula da ofishin hukumar dake Sokoto Aliyu Shehu ya ce yanzu aka fara bada tallafin kasancewar hukumar ta yi tsare tsare na kawo tarin agaji ga wadanda iftila’in ya shafa.

Kayan da aka raba sun hada da kayan abinci,littattafai ga dalibai,tabarmi da sauran kayan amfanin yau da kullum.

NEMA ta rabawa wadanda ambaliya ta shafa a Zamfara tallafi

NO COMMENTS