Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya sanar da bawa ma’aikatan gwamnati N150,000 domin taya su murnar bikin krisimeti.
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Monday Uzor, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin Facebook ranar Alhamis da daddare.
A cewar Uzor, ma’aikatan jihar za su karɓi wannan garabasar kafin karfe 1 na rana a ranar Talata, 17 ga Disamba, 2024.
“Duk ma’aikaci a jihar Ebonyi zai karɓi Naira 150,000 a matsayin garabasar Kirsimeti kafin karfe 1 na rana a ranar Talata… Gwamna Rt. Hon. Francis Ogbonna Nwifuru,” inji sanarwar.
Gwamnan Ebonyi ya baiwa ma’aikatan jihar N150,000 don bikin kirsimeti