Majalisar Dokokin Jihar Adamawa ta bayyana cewa Lamidon Adamawa har yanzu shi ne Shugaban Majalisar Sarakuna da Hakimai ta jihar.
Shugaban Kwamitin Bayar da Bayanai na Majalisar, Musa Mahmoud Kallamu, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a ranar Juma’a, inda yace dokar Majalisar Sarakunan Jihar Adamawa ta tabbatar da matsayin Lamidon Adamawa a matsayin shugaban majalisar.
A cewar Kallamu, Sashe na 17 na dokar ne ya kafa Majalisar Sarakunan Jihar Adamawa, yayin da Sashe na 18 ya bayyana mambobin majalisar, wadanda suka haɗa da sarakuna, hakimai masu daraja ta biyu, babban sakataren harkokin masarautu, da kuma shugaban ALGON.
Kallamu ya jaddada cewa matsayin Lamido Adamawa na shugaban majalisar bai canza ba duk da kirkiro sabbin masarautu da aka yi. Wadanda a tsakaninsu zasu dinga shugabanci na juyi-juyi, amma za su riƙa kai rahoto ga shugaban majalisar jihar, wato Lamidon Adamawa.
Har yanzu Lamidon Adamawa ne shugaban majalisar Sarakuna – Majalisar dokoki