Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke umarnin da aka bayar wanda ya hana Babban Bankin Najeriya (CBN) da Akanta Janar na Tarayya tura kudade ga gwamnatin jihar Ribas.
Alkalan uku, karkashin jagorancin Mai Shari’a Hamman Barka, ya yanke hukuncin cewa batun kudaden shiga na jiha ba ya cikin hurumin kotun da ta bayar da umarnin farko.
Kotun ta kuma tabbatar da daukaka karar da gwamnatin Jljihar Ribas ta shigar, inda ta soke umarnin da Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta bayar a baya.
Kotun ta bayyana umarni a matsayin wanda baya bisa doka ba, kuma ya tauye hakkin gwamnatin ihar Ribas na samun damar amfani da kudaden ta daga asusun hadaka na tarayya.
Haka kuma, kotun daukaka kara ta zargi kotun baya da ketare iyaka, tana mai cewa ba ta da hurumin sauraren wannan batu.
Daily Post Hausa ta ruwaito cewa a watan Oktoba, Mai Shari’a Abdulmalik ta babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci cewa karba da rabon kudaden jihar da vwamna Siminalayi Fubara, ya ke yi tun daga watan Janairu ya saba wa tanadin doka.
Mai shari’ar ta kuma bayyana gabatar da kasafin kudin 2024 da gwamnan ya yi a gaban ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas guda hudu a matsayin abinda ya saba wa kundin tsarin mulkin 1999.
Bayan haka, Mai Shari’a Abdulmalik ta bayar da umarnin hana CBN, Akanta Janar na Tarayya, bankin Zenith, da Bankin Access ba wa Fubara damar amfani da kudade daga Asusun Tarayya, Sai dai yanzu kotun daukaka Karar ta soke wadannan hukunce hukunce.
Kotu ta soke hukuncin da ya hana jihar Ribas kudadenta