SHARE

Hafsan tsaron kasar nan (CDS), Janar Christopher Musa, ya tura rundunarayyukan .usamman zuwa jihohin Sokoto da Kebbi a matsayin wani bangare na kokarin kawar da kungiyar Lakurawa daga yankin.

A cewar wata sanarwa da aka fitar a Sokoto, an tura rundunar ne don karfafa nasarorin da aka samu karkashin Ayyukan Forest Sanity III, wanda aka rada wa suna Chase Lakurawas Out.

Da yake jawabi ga sojojin a ranar Juma’a, Birgediya Janar Ibikunle Ajose, kwamandan runduna ta 8 na rundunar sojin Najeriya da kwamandan Sector 2, rundunar Fasan Yamma, ya isar da umarnin kwamandan Theatre, Manjo Janar Oluyinka Soyele.

Ya umarci sojojin da su tabbatar da rushe kungiyar Lakurawa gaba daya a jihohin da abin ya shafa.

Birgediya Janar Ajose ya bukaci sojojin da su bi ka’idojin aiki sosai yayin da suke mayar da hankali kan kare rayuka da dukiyoyin al’ummar da ba su da laifi.

Ya jaddada cewa an zabo rundunar ta musamman bisa tsari sannan an ba ta horo na musamman don wannan aiki, tare da nuna tabbaci a kan kwarewarsu da iyawarsu.

“Yan Najeriya suna dogaro da kwarewarku wajen kawar da kungiyar tare da dawo da zaman lafiya,” in ji shi.

Kwamandan rundunar ya bayyana ayyukan da suka gabata na tsara dabaru da sojojin runduna ta 8 suka gudanar karkashin Fasan Yamma.

Wadannan ayyuka sun shafi dazuzzuka da mafakar yan kungiyar a wurare kamar Rumji Dutse, Sarma, Tsauna, Bauni, Malgatawa, Gargao, Magara, Kaideji, Nakuru, Sama, Sanyinna, Kadidda, Kolo, da Dancha a cikin kananan hukumomi irin su Illela, Tangaza, da Binji.

Rahotanni sun nuna cewa wadannan ayyuka sun haifar da rushe sansanoni 22, kashe mambobin kungiyar da dama, da kuma karbe makamai, ciki har da bindigogi hudu, harsasai 409 na PKT 7.62mm NATO, da kuma harsasai 94 na 7.62mm na musamman.

“Tura Rundunar Ayyukan Musamman zai zama karin karfi don dakile ayyukan ‘yan bindigar, wanda zai dawo da zaman lafiya a al’ummomin da abin ya shafa da kuma yankin Arewa maso Yamma baki daya,” in ji Birgediya Janar Ajose.

Lakurawan: Rundunar soji ta aika dakaru na musamman zuwa jihohi 3

NO COMMENTS