A yayin bikin Ranar Kula da Lafiya ga Kowa (UHC) ta duniya, Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano tare da Hukumar Kula da Tsarin Kiwon Lafiya ta Contributory Healthcare Management Agency (KSCHMA), sun bayyana ci gaban da aka samu wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya ga dukkan al’ummar Jihar Kano.
A jawabin Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya ce
Taken bana na UHC, “Lafiya Amanar Gwamnati,” ya jaddada aniyar gwamnati na fadada damar samun ingantaccen kiwon lafiya ga jama’a.
“Jihar Kano itace mai mafi yawan al’umma a Najeriya, kuma hakan yana kawo kalubale a fannin kiwon lafiya.
“Idan ba a dauki matakai masu inganci ba, wannan yawan zai iya zama matsala maimakon albarka. Muna yin aiki tukuru don ganin kowanne dan Jihar Kano ya samu kiwon lafiya ba tare da wahalar kudi ba.”
A yayin taron, Dr. Rahila Aliyu Mukhtar, Sakatariyar Hukumar KSCHMA, wacce ke halartar wata muhimmiyar ganawa a birnin tarayya Abuja, tace, KSCHMA tana gudanar da shirye-shirye uku masu muhimmanci domin tabbatar da an samar da kula da lafiya ga ma’aikata, ‘yan kasuwa, da masu bukatar tallafi
Hukumar KSCHMA ta bayyana cewa ta samu nasarar yin rijistar mutum 934,676, ciki har da 281,600 daga cikin masu rauni, a karkashin shirin kiwon lafiya na contributory.
Hakazalika, an kafa tsarin kula da masu fama da cutar sikila, inda aka yi rijistar marasa lafiya sama da 10,000 karkashin shirin ABBACARE.
“KSCHMA tayi fice wajen shirin ABBACARE don kula da masu fama da cutar sikila, inda aka yi wa marasa lafiya fiye da 10,000 rajista daga cikin 39,000 da ake niyya. Haka zalika, an kula da marayu 470, masu bukata ta musamman 15,983, masu fama da cuta Mai karya garkuwar jiki 3,639, da masu cutar hawan jini da sikari sama da 2,374.
Hukumar ta kuma bada kulawa ga mata masu juna biyu fiye da 120,000, wanda ya kai ga haihuwar yara 21,264 cikin lafiya da kuma tiyatar haihuwa 1,220.
Haka kuma, Hukumar ta biya kudin maganin cutar zazzabin cizon sauro 1,500,000, cutar amai da gudawa 63,842, da cututtukan numfashi fiye da 204,000.
Dr. Rahila ta kara da cewa, “An riga an yi gwajin mutum 47,289 da ke fama da hauhawar jini, inda 6,948 suka samu kulawa. Haka zalika, mutum 20,760 sun yi gwajin ciwon suga, daga ciki kuma 7,464 sun samu magani.”
Dr. Rahila ta tabbatar wa mazauna Kano cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da aiki tukuru don inganta lafiyar al’umma tare da kare jin dadin su.
“Muna tabbatar wa kowa da cewa karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf, Ma’aikatar Lafiya da dukkan hukumomin ta za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an cimma manufofin UHC,” in ji ta.
A ƙarshe, ta taya Kwamishinan murna bisa sake naɗa shi don cigaba da jagorantar ma’aikatar lafiya, tana mai cewa, “Wannan amincewa alama ce ta kwazon ku wajen sauke nauyin da aka dora muku.”
Kano: Ma’aikatar lafiya da KSCHMA sunyi alkawarin ci gaba da bunkasa tsarin kula da lafiya