SHARE

Shugaban ƙasar Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol, ya fuskanci cirewa daga mukaminsa.

A ranar Asabar, majalisar dokokin Koriya ta Kudu ta kada kuri’ar tsige Yoon daga mukaminsa.

Cire shi ya biyo bayan yunƙurinsa na kafa dokar soja, matakin da ya girgiza al’umma kuma ya haifar da rarrabuwar kai a jam’iyyarsa.

Al Jazeera ta ruwaito cewa mambobin majalisar dokokin Koriya 204 sun zabi goyon bayan tsige Yoon, yayin da 85 suka zabi kin amincewa da tsige shi.

An hana Yoon tafiye-tafiye zuwa kasashen waje yayin da ake gudanar da bincike a kansa.

An cire Shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol, daga mukaminsa

NO COMMENTS