in

Sojoji sun lalata sansanoni 22 na Lakurawa

Dakarun Operation Fansan Yamma sun lalata sansanoni 22 na yan ta’addan Lakurawa tare da kashe da dama daga cikinsu a jihar Sokoto.

Sojojin sun kwato makamai da alburusai yayin samamen.

Mukaddashin babban kwamandan runduna ta 8 kuma kwamandan sashi na 2 na Operation Fansar Yamma, Birgediya Janar Ibikunle Ajose ne ya bayyana hakan, a lokacin da yake jawabi ga runduna ta musamman da aka tura domin murkushe Lakurawa a jihohin Sokoto da Kebbi.

A cewarsa, tura Bataliyar zai zama wani karin kaimi wajen dakile ayyukan ‘yan ta’adda da kuma dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma baki daya.
Sai dai ya bukaci sojojin da su tabbatar da lalata kungiyar ta Lakurawas gaba daya.

Ya umarce su da su bi ka’idojin aiki tare da tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa masu bin doka da oda.

Sojoji sun lalata sansanoni 22 na Lakurawa

Gwamna Sani ya nada sabon mai ba shi shawara kan harkokin karkara

Bafarawa ya ƙaddamar da gwagwarmayar ceto Arewa