Kungiyar malaman kwalejin fasaha ta kasa (ASUP), ta dakatar da yajin aikin gargadi na makonni biyu da ta fara, inda ta umarci mambobinta su koma aiki a ranar Litinin, 16 ga Disamba, 2024.
DAILY POSY hausa ta ruwaito cewa, yajin aikin da aka fara a ranar 2 ga Disamba, 2024, an kaddamar da shi ne don nuna adawa da yadda yi watsi da kwalejojin fasaha a Najeriya da sauran matsaloli.
A cewar Shugaban kungiyar ASUP na kasa, Shammah Kpanja, shawarar dakatar da yajin aikin ta biyo bayan ganawa da Ma’aikatar kwadago.
An sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MOU), kuma za a kara zama wani taron nan gaba a ranar 23 ga Janairu, 2025, don warware rikicin.
Kwamitin zartarwa kungiyar ASUP zai duba halin da ake ciki kafin taron na Janairu.
ASUP ta bayyana cewa, yajin
ya kasance a matsayin gargadi don yin Allah wadai da yadda gwamnatin tarayya ta kasa aiwatar da abubuwa tara na ka’idodin aiki da aka tsara da kungiyar.
ASUP ta janye yajin aiki