Tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano, Dr. Abdullahi Baffa Bichi, ya kai wa tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ziyara.
Dr. Bichi ya kai ziyarar ne bayan gwamnatin Kano ta sauke shi daga mukaminsa na sakataren gwamnatin jihar a ranar Alhamis bisa cewa zai je neman lafiya.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sauke Dr. Bichi tare da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano, Malam Shehu Wada Sagagi, da wasu kwamishinoni biyar, tare da sauya wuraren aikin wasu kwamishinoni.
Ba a kai ga bayyanawa manema labarai cikakken bayani a kan abubuwan da Malam Ibrahim Shekarau da Dr. Abdullahi Baffa Bichi suka tattauna ba.
Sai dai ana has ashen cewa Dr. Abdullahi Baffa Bichi na iya komawa bangaren Malam Ibrahim Shekarau a jam’iyyar adawa ta PDP, yayin da wasu ke zargin cewa zai iya komawa bangaren Sanata Barau I. Jibril a cikin APC.
Tsohon sakataren gwamnatin Kano ya ziyarci Shekarau