Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanya hannu kan doka da ta haramta satar sassan jiki na mutane, tare da hukuncin shekaru 10 na kurkuku ga wadanda aka samu da laifi.
Dokar Hana Satar Sassan Jiki ta kasance daya daga cikin sabbin dokoki guda biyar da gwamnatin jihar ta kaddamar a makon da ya gabata.
Sanwo-Olu ya bayyana sanya hannun sa kan wadannan dokoki a matsayin shaida ga jajircewar gwamnatin jihar wajen tabbatar da walwala, tsaro, da ci gaban kowane dan Legas.
Bayan dokar cinikayyar sassan jikin dan adam da dashensu, sauran dokokin da Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sanya hannu sun hada da Dokar Horas da Ma’aikatan Hukumar Tilasta Dokoki ta Jihar Legas, Dokar Tallafa wa Wanda aka ci zarafinsu da Kare Shaidu, da kuma Dokar Hukumar Kashe Gobara da Ceto ta Jihar Legas.
Sanwo-Olu ya amince da hukuncin shekaru 10 ga masu safarar sassan jiki