in

Matatar Dangote ta fara fitar da man fetur zuwa kasashen Afrika

Matatar Man Fetur ta Dangote ta fara fitar da man fetur (PMS) zuwa kasashe kamar Kamaru, Ghana, Angola, da Afirka ta Kudu.

Dr. Devakumar Edwin, Mataimakin Shugaban Harkokin Man Fetur da Gas na Dangote Industries Limited, ya bayyana hakan me a yayin wata ziyarar da Jakadan Japan mai jiran gado a Najeriya, Suzuki Hideo, da wani tawaga daga al’umma kasuwancin Japan suka yi.

Dr. Edwin ya jaddada karuwar tasirin matatar a duniya, inda ya ce, “A cikin makonni kadan da suka gabata, mun fara fitar da man fetur zuwa kasashen Afrika da dama.”

“Man dizal ɗinmu yana isa kasuwanni a duk duniya, kuma man jirgin sama na samun karbuwa a Turai. Wadannan fitarwar suna nuna gasa na kasa da kasa na kayayyakinmu.”

Ya nuna muhimmancin rawar da matatar ke takawa, wanda nufinsa shine bunkasa masana’antu, samar da ayyukan yi, da kuma inganta ci gaban tattalin arziki.

Tawagar Japan ta yabawa matatar a matsayin alama ta ci gaban masana’antu da fasaha na Najeriya.

Matatar Dangote ta fara fitar da man fetur zuwa kasashen Afrika

NPFL: Lönnström hails Lobi Stars’ display vs Plateau United

Gwamna Buni ya kafa ma’aikatar kula da kiwo dabbobi a Yobe