Wani mutum ya rasa ransa bayan ya banka wa kansa da matarsa wuta a unguwar Ijoka da ke Akure, babbar birnin Jihar Ondo.
Lamarin ya faru ne bayan rikici ya barke tsakanin ma’auratan kan batun aurensu.
Ma’auratan sun shafe kusan shekaru 20 tare, tare da haihuwar ’ya’ya biyu, amma rikici yasa mijin ya bar zama tare da matar a watannin baya, kamar yadda wasu makusantansu suka bayyana.
Rahotanni sun nuna cewa mijin ya aikata wannan ɗanyen aiki ne bayan duk ƙoƙarinsa na sulhu da matar bai yi nasara ba. Jami’an tsaro sun ce mutumin ya gayyaci matar ne zuwa gidansa da nufin karɓar wasu kaya, amma daga bisani ya rufe dakin, ya watsa fetur, sannan ya banka musu wuta.
Mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Ondo, Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da faruwar lamarin. Ta ce mijin ya mutu a wurin, yayin da matar aka garzaya da ita asibiti domin ceto rayuwarta.
A cewarta, “Bayan samun sabani, mijin ya kira matar don ta karɓi wasu kaya. Amma daga bisani ya fara barazanar kashe kansa. Ya rufe dakin, ya watsa fetur, sannan ya kunna wuta. Shi ya mutu nan take, amma matar na karɓar kulawa a asibiti.”
Wani Mutum ya bankawa Kansa da Matarsa wuta a Ondo