Shugaban Kasar Ghana mai jiran gado, John Dramani Mahama, ya kawo ziyara ga Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban kasa dake Abuja.
Bayanin hakan ya fito ne daga mai taimaka wa Tinubu kan harkokin kafafen sada zumunta, Dada Olusegun, a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata.
Inda ya ce, “zababben shugaban kasar Ghana, H.E John Dramani Mahama, ya kai ziyarar ban girma ga Shugaba Tinubu a fadar Shugaban Kasa a jiya.”
Wannan ziyarar ta biyo bayan sakon taya murna da Tinubu ya aika wa Mahama bayan nasararsa a zaben shugaban kasar na ranar 7 ga Disamba.
DAILY POST ta ruwaito cewa Tinubu, a cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da Mahama, ya bayyana fatan dawowarsa kan mulki zai karfafa zaman lafiya a Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).
Har ila yau, ya nuna sha’awarsa na yin aiki tare da sabuwar gwamnatin Mahama don karfafa dangantaka a fannoni daban-daban da kuma yin aiki domin makoma mai kyau ga yankin yammacin Afirka.
Zababben shugaban Ghana ya ziyarci Tinubu