Shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio, ya ce gwamnatin Najeriya za ta tsawaita wa’adin kasafin kudin shekarar 2024 har zuwa watan Yuni na shekarar 2025.
Akpabio ya yi wannan sanarwa a ranar Laraba yayin zaman hadin gwiwa na majalisar tarayya.
Ya bayyana cewa ana ci gaba da zaman domin daukar matakin aiwatar da tsarin tsawaita kasafin a yanzu.
“Duba da wadannan manyan nasarori, mun ga dacewar tsawaita wa’adin kasafin kudin 2024 zuwa 30 ga Yuni, 2025.
Akpabio ya kara da cewa tuni ‘yan majalisa su ka bijiro da dokar da ta amince a yi irin wannan tsawaitawar saboda muhimmancinsa ga ci gaban kasa.
Gwamnati za ta tsawaita wa’adin kasafin kudin 2024 zuwa 2025