Segun Olowookere, wanda ya shafe shekaru 10 a gidan yari yana jiran a zartar masa da hukuncin kisa saboda satar kaji, zai samu ‘yanci bayan gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi alƙawarin yi masa afuwa.
A shekarar 2010, Olowookere yana da shekara 17 lokacin da aka kama shi tare da wani mutum mai suna Morakinyo Sunday. Ana zargin su da kai hari a gidan wani ɗan sanda da kuma gidan wani farar hula, inda suka sace kaya daga gidan gona tare da ɓoye tsohuwar bindiga.
A cikin 2014, Mai Shari’a Jide Falola na Babbar Kotun Jihar Osun ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan da aka same su da laifin yin sata a gidan ɗan sandan. Wannan lamari ya jawo hankalin mutane a Najeriya, inda aka yi ta muhawara kan tsananin hukuncin.
A cikin wata sanarwa a ranar Talata, gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya umarci a yi wa Olowookere afuwa. Ya bayyana cewa: “Na bayar da umurnin kwamishinan shari’a ya fara aikin afuwar wannan matashi. Osun jihar adalci ce, kuma dole ne mu tabbatar da cewa ana aiwatar da adalci tare da kare rayukan al’umma,” gwamnan ya rubuta a shafinsa na X.
Sai dai, ba a san abin da zai faru da Morakinyo Sunday ba, wanda aka yanke masa hukuncin kisa tare da Olowookere, saboda ba a ambaci sunansa a cikin sanarwar ba.
A cikin waɗannan shekaru, iyayen Olowookere, ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama, da sauran ‘yan Najeriya sun yi ƙoƙari sosai don ganin an sako shi. Iyayensa sun bayyana cewa shi ne kaɗai ɗansu, don haka ya kamata a yi masa afuwa.
Ana sa ran Olowookere zai samu ‘yanci a farkon shekarar 2025.
Za a yiwa barawon kajin da aka yankewa hukuncin kisa afuwa