in

Kano: Gwamna Abba ya zargi jam’iyyun adawa da hannu a ta da tarzoma

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya zargi wasu mambobin jam’iyyun adawa da haddasa tarzoma da rashin zaman lafiya a jihar.

Gwamnan ya bayyana wannan zargi ne a ranar Laraba yayin taron majalisar zartarwa ta jiha, inda ya ce rikicin baya-bayan nan tsakanin wasu matasa ‘yan daba a tsakiyar birnin Kano ya samo asali ne daga masu ɗaukar nauyin fitintinu.

A cewarsa, rahoton sirri da aka tattauna a taron kwamitin tsaro na jiha a ranar Talata ya bayyana sunayen waɗanda ke da hannu a tashe-tashen hankulan.

Gwamna Yusuf ya ce jam’iyyun adawa ba su farin ciki da zaman lafiya da cigaban da jihar ke rura wutar rigingimun.

Duk da haka, gwamnan ya yi alkawarin ɗaukar matakan gaggawa don kawo ƙarshen dawowar ayyukan ‘yan daba a jihar.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yarda wani ya yi ƙoƙarin dagula zaman lafiya a Kano ba.

Ya kuma tabbatar da cewa za su haɗa kai da hukumomin tsaro don magance ayyukan masu tayar da hankali a jihar.

Gwamnan ya sanar da shirye-shiryen sake buɗe cibiyar gyaran hali da ke karamar hukumar Kiru domin sake tarbiyyar matasa da kuma dakile amfani da miyagun ƙwayoyi a jihar.

Haka zalika, Yusuf ya bayyana aniyar gwamnati ta kaddamar da sabuwar majalisar Shura ta malamai 46, wadda ta ƙunshi manyan malamai na addini, masana, da sauran masu ruwa da tsaki, domin ci gaban jihar.

Kano: Gwamna Abba ya zargi jam’iyyun adawa da hannu a ta da tarzoma

Livestock reform will boost economy, address food security challenges – Prof Jega

Okpebholo’s Asset recovery committee storms Election Petitions Tribunal to recover vehicle