Yayin da ya rage saura kasa da sati daya a fara bukukuwan Kirsimeti da kuma makonni biyu zuwa Sabuwar Shekara, farashin tikitin jiragen sama zuwa yankin Kudu Maso Gabas ya yi tashin gwauron zabo, inda tikitin dawowa ke kai wa sama da N700,000.
Binciken da aka yi a shafukan yanar gizon kamfanonin jiragen sama kamar Air Peace, United Nigeria Airline, Ibom Air, Arik, da Aero Contractors ya nuna cewa farashin tikitin zuwa jihohin Anambra, Enugu, Owerri da Fatakwal ya yi matukar tashi.
Masana sun bayyana cewa wannan karin farashi ya samo asali ne daga yawan bukatar kujeru, kasancewar jihohin Kudu Maso Gabas jihohi ne da mafi yawan mazaunansu kiristoci, kuma suna bawa bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara mahimmanci.
Haka kuma, rashin tsaro da fargabar sace mutane a hanya ya sa matafiya suna fifita amfani da jirgin sama domin zirga-zirga sama da bin titi.
Farashin tikiti ya nuna cewa jirgin United Nigeria Airline daga Legas zuwa Anambra na kaiwa N700,000, yayin da jirgin Air Peace zuwa jihar Anambra yana kan N672,900.
Masu sharhi a bangaren sufuri sun bayyana cewa tashin farashin jiragen sama ya sa wasu matafiya sun koma amfani da motocin haya.
Farashin tikitin jirgin sama zuwa yankin kudu maso gabas ya doshi kaiwa 1mn gabannin bukukuwan kirsimeti