in

Jihar Kano ta yi zarra a gasar Noma ta kasa ta 2024

Jihar Kano ta zama zakara a gasar noma ta kasa ta 2024, wadda aka gudanar a Jihar Nasarawa.

Bugu da ƙari, Kano ta samu matsayi na biyu a fannin kiwon kifi a gasar da aka kammala kwanan nan.

Sanarwar da mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba ta bayyana cewa an mika kambun lashe gasar ga gwamnan ta hannun Kwamishinan ma’aikatar Noma da albarkatun kasa, Dakta Danjuma Mahmud, yayin taron Majalisar Zartarwa ta Jiha karo na 22.

Gwamna Yusuf ya yabawa ma’aikatar noman bisa wannan nasara, yana mai jinjina wa Dakta Mahmud bisa jagoranci nagari.

Ya kuma bukaci ma’aikatar da ta ci gaba da gudanar da ayyuka masu nagarta tare da kira ga sauran ma’aikatu su yi koyi da wannan kokari wajen samar da ayyukan cigaba ga al’umma.

Jihar Kano ta yi zarra a gasar Noma ta kasa ta 2024

EPL: It was harsh – Neville regrets comment about ex-Chelsea, Arsenal star

Zamfara Gov’s wife marries off 100 orphans, provides assistance to grooms