in

Kotu ta yankewa wani mutum hukuncin kisan ta hanyar rataya a Kano

Wata babbar kotun jihar Kano mai lamba 7 dake sakatariyar Audu Bako, ta yankewa wani mutum hukuncin kisan ta hanyar rataya.

Alkalin kotun, maisharia Amina Adamu, ta yankewa Abba Sulaiman hukuncin, saboda samunsa da laifin hada kai, da kuma kisan wani Tasi’u Ilyasu, ta hanyar caka masa wuka.

Lamarin ya faru ne a unguwar Sauna Kawaji tun a shekarar 2019, bayan wani rikici da ya barke tsakanin dangin wata amarya da uwargidanta, sakammakon zargin dangin uwargidan na hana a shigar da amaryar gidanta, al’amarin da ya kai ga wancan kisa.

Yayin shari’ar, mai gabatar da kara, Barista Usman Abdullahi Usman, ya nuna shaidu biyu, inda lauyan wanda ake kara, Barista Auwal Abubakar Ringim, ya gabatar da wanda ake zargi, kuma ya kare kansa.

Da take yanke hukunci, maisharia Amina Adamu, ta ce ta gamsu da shaidun da masu kara suka gabatar, da hakan ya sa ta yankewa mai laifi hukuncin daurin shekaru biyar a tuhumar farko ta hada-kai, inda bisa laifin kisa kuma, ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Bayan fitowa daga kotu, lauyan masu kara, wanda kuma shi ne lauyan gwamnatin Kano, Barista Usman Abdullahi Usman, ya ce sun gamsu da hukuncin.

Shi kuma lauyan wanda aka yankewa hukunci, Barista Auwal Abubakar Ringim, ya ce za su yi nazarin hukuncin domin daukar mataki na gaba.

Kotu ta yankewa wani mutum hukuncin kisan ta hanyar rataya a Kano

Bikin Kirsimeti: NSCDC ta tura jami’ai 4,000 FCT

Transfer: ‘Agreement is close’ – Romano confirms Bundesliga club to sign Nigerian striker