in

56% na yan Najeriya na son ficewa daga kasar – Bincike

Kashi 56 cikin 100 na al’ummar Najeriya sun bayyana sun bayyana aniyarsu ta ficewa daga kasar, wanda ke nuna karin kashi 20 idan aka kwatanta da adadin mutanen da suka yi irin wannan tunanin a 2017, wanda ya kasance kashi 36 cikin 100, a cewar rahoton Afrobarometer, wata cibiyar bincike ta pana-Afirka, ta fitar

Kason yafi yawa tsakanin masu ilimi sosai. Wadanda ke da takardar shaidar karatu bayan matakin sakandare, sune kashi 71% na yawan masu kokarin ficewar, yayin da mazauna birane da matasa suka haura kashi 60 cikin 100.

Afrobarometer ta nuna cewa neman damar inganta rayuwa, damar aiki, da guje wa talauci ko matsalar tattalin arziki sune manyan dalilan da ke sa ‘yan Najeriya son barin kasar, inda ta ce “dalilan da aka fi ambata na son yin hijira sun hada da neman damar aiki (42%) da guje wa talauci ko wahalar tattalin arziki (39%).”

Kasashen da ‘yan Najeriya ke son zuwa sun fi yawa a Arewacin Amurka, Turai, da Gabas ta Tsakiya.

A cewar rahoton, kashi biyu daga cikin kashi uku (66%) na mutanen da aka dauka daga cikin wadanda ba su da aiki kuma suna neman aiki sun yi tunanin barin Najeriya.

A bangare guda, yawancin ma’aikata na cikakken lokaci (58%) da na lokaci-lokaci (56%) ma sun yi tunanin hijira.

Karuwar hijira ta haifar da raguwar kwararru, musamman a fannin kiwon lafiya, domin yawancin ma’aikatan lafiya suna barin kasar don neman ingantataccen yanayin aiki a wasu kasashen.

56% na yan Najeriya na son ficewa daga kasar – Bincike

Customs intercepts foreign rice, cannabis sativa, others worth N229m in Ogun

Troops arrest illegal miners, recover mined products in Taraba