Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana farin cikinsa game da amincewar kamfanin haƙar mai na Shell da abokan hulɗarsa wajen zuba jarin dala biliyan biyar a wani babban aikin haƙo ɗanyen mai daga teku.
Rahotonni sun ce aikin haƙar man zai kasance na farko cikin shekaru da dama a Najeriya, kuma zai tallafawa manufofin shugaban ƙasa na jawo hankalin masu zuba jari a fannin mai da iskar gas. Aikin, wanda aka sa wa suna ‘Bonga North Oilfield’, zai samar da dala biliyan biyar, tare da samar da gangar ɗanyen mai miliyan 350.
Kamfanin Shell yana da kaso 55% na gudanar da wannan aiki, yayin da sauran abokan hulɗar da suka haɗa da NNPC, ExxonMobil, TotalEnergies, da Eni.
Bugu da ƙari, aikin zai taimaka wajen bunkasa fannin wutar lantarki.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa “shirin sabunta fata ya maida hankali kan jawo hankalin masu zuba jari domin inganta tattalin arziƙi da samar da wadata da cigaba ga al’umma.
Kamfanin Shell zai saka jarin Dala biliyan 5 a Najeriya