Kungiyar Tsoffin Daliban Makarantar GGSS Dala ta gina katafariyar cibiyar koyon sana’o’i a Makarantar GGC Dala Kano domin koyar da ɗalibai sana’o’in da za su dogara da kansu.
Shugabar kungiyar, Hajiya Saudatu Sani, ta bayyana haka a taron manema labarai wajen taron shekara-shekara na kungiyar a ranar Alhamis.
Hajiya Saudatu ta ce, tsawon shekara guda kungiyar ta kasance tana aiki ba dare ba rana domin magance matsalolin da suka addabi makarantar tun tsawon lokaci.
Ta bayyana cewa, a cikin wannan lokacin, sun gyara ajujuwa fiye da arba’in, gina rijiyoyin burtsatse, samar da kujeru da teburan karatu, da kuma yin katanga domin inganta tsaron makarantar.
Hajiya Saudatu ta kuma bayyana cewa, tare da goyon bayan dattijon ƙasa kuma attajiri, Alhaji Aminu Dantata, sun tara fiye da Naira miliyan 160 domin gyaran makarantar.
“Mafi yawan matsalolin da suka dabaibaye makarantar GGC Dala yanzu sun zama tarihi, musamman matsalar tsafta da ruwan sha, saboda yanzu akwai wadataccen ruwa da tsafta. Kujeru da tebura sun wadatu,” in ji ta.
“Mun ƙaddamar da horar da malamai kan sabbin dabarun koyarwa, kuma wannan cibiyar koyon sana’o’in za ta taimaka wa ɗalibai wajen samun ƙwarewa kafin su kammala makaranta.”
Hajiya Saudatu ta koka kan halin da gidan malamai na makarantar ke ciki, inda ta ce wadanda ba ma’aikatan makarantar ba ne suke zaune a wurin, lamarin da ke kawo barazana ga makarantar, wanda ya sa dole a gina katanga.
Tsofaffin daliban GGC Dala sun ginawa makarantar cibiyar koyon sana’a