Ministan Shari’a kuma Shugaban Hukumar Shari’a ta Tarayya, Prince Lateef Fagbemi (SAN), ya ce dakatar da shugabannin kananan hukumomi da mataimakansu a Jihar Edo ba daidai ba ne kuma ya saba da doka.
AGF ya tabbatar da hakan a cikin wata hira da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa wannan matakin ya saba da ‘yancin kananan hukumomi da kotun koli ta tabbatar a cikin hukuncinta na 11 ga Yuli, 2024.
Harkallar ta taso ne bayan Majalisar Dokokin Jihar Edo ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi daga dukkanin LGAs 18 na jihar na tsawon wata biyu, tana zargin su da aikata manyan laifuka da kuma kin bin dokoki.
Gwamna Monday Okpebholo ya bi sahun wannan matakin da umurnin da ya baiwa shugabannin kananan hukumomi su mika ragamar mulki ga shugabannin majalisu na yankunan su, yana zarginsu da kin gabatar da rahotannin kudade tun daga ranar 23 ga Satumba, 2022.
Duk da haka, jami’an da abin ya shafa sun ki amincewa da umarnin dakatarwa, suna mai da hankali kan niyyarsu taci gaba da aiki harsai lokacin karshen wa’adin su a 2026.
AGF ya bayyana cewa kawai majalisun kananan hukumomi ne ke da ikon hukunta shugabanninsu.
“Abu guda da na sani kuma zan iya fada ba tare da tsoro ba shi ne cewa, a cikin wannan gwamnatin, gwamna ba shi da hakkin sauke kowanne shugaba na karamar hukuma,” in ji Fagbemi.
AGF: Dakatar da shugabannin kananan hukumomin Edo ba daidai ba ne