Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴan Sandan Nijeriya, Olumuyiwa Adejobi, ya yi Allah wadai da ɗabi’ar zagin mutane kai tsaye a yanar gizo, yana mai jaddada cewa irin wannan hali na janyo a hukunta mutum.
A wata sanarwa da ya wallafa a X.com a ranar Juma’a, Adejobi ya bayyana cewa yin amfani da munanan kalamai wajen zagi ko cin zarafin wani a yanar gizo ya zarce iyakar ‘yancin faɗin albarkacin baki ko sukar wani.
Ya rubuta cewa, “Zagin mutum kai tsaye a yanar gizo cin zarafi ne, ba ‘yancin faɗin albarkacin baki bane.
“Kuma cin zarafi ta yanar gizo, wanda ya sha bamban da ɓata suna, laifi ne kuma ana iya hukunta mutum. A yi hattara.”
Olumuyiwa Adejobi: Zagi kai tsaye a yanar gizo cin zarafi ne