Asusun kula da yara kanana na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa Najeriya na cikin jerin ƙasashen duniya da yawan yaran dake kasa zuwa makaranta ke da tsanani.
Asusun ya gano babban dalilin haka ya ta’allaka ne kan rikice-rikice da matsalar rashin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.
Wannan lamari ya jawo hankalin masu ruwa da tsaki, inda hakan ta sa aka fara daukar mataki.
A wani yunƙuri don magance wannan matsala, wata mata a jihar Filato ta kafa gidauniya ta musamman a wani ƙauye, bayan da iyalai da dama suka gaza biyan kuɗin makarantar yaransu.
Ta hanyar wannan gidauniya, ana wayar da kai tare da tallafa wa yara domin samun damar zuwa makaranta.
UNICEF ta yi takaicin yawan yara marasa zuwa makaranta a Najeriya