An kaddamar da allurar rigakafin zazzabin cizon sauro tun bayan karbar allurar a rigakafin a watan Oktobar daya gabata.
Rigakafin mai suna R21/Matrix-M shine nau’in rigakafin malaria karo na biyu dahukumar lafiya ta amince da shi domin amfanin yara yan tsakanin watanni 15 zuwa shekaru biyar.
Ana sa ran zai magance kaso 75 cikin dari daga cikin matsalolin da cutar zazzabin cizon sauro ke haifar wa hakan yasa aka fara allurar a jihohin Bayelsa da Kebbi da sukafi kowace jiha fama da cutar.
Nijeriya ce dai kasar da ke da kashi 27 cikin 100 na masu dauke da cutar zazzabin cizon sauro a duniya. Sannna kasar na da kuma kashi 31 na wadanda cutar ke kashewa a duniya, kamar yadda rahoton malaria na duniya na 2023 ya nuna.
Akalla mutum 200,000 ne suka rasu a sanadiyar cutar zazzabin cizon sauro a shekarar da ta wuce. Hakazalika, yara ‘yan kasa da shekara biyar da mata masu ciki ne suka fi saurin kamuwa.
Za’a fadada rigakafin zuwa wasu jihohin nan da wasu watanni masu zuwa.
A karan farko a tarihi an fara rigakafin zazzabin cizon sauro a Najeriya