Ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore ta ayyana 13 ga watan Disamba a matsayin Ranar Shan Fura ta Duniya domin farfaɗo da al’adun Fulani a Nijeriya da dama duniya baki ɗaya.
Sai dai kuma bikin na zuwa ne a daidai lokacin da sojoji suke tsare da Bello Boɗejo wanda suka kama a gidansa a makon jiya, ba tare da sun bayyana dalilin kama shi ba.
A kwanakin baya kafin a kama Shugaban ƙungiyar shugaban kungiyar, Alhaji Bello Badejo, ya bayyana cewa sun shirya tsaf domin kaddamar da bikin ranar wadda daga bana za a ci gaba da yi domin farfaɗo da kyawawan al’adu na Fulani.
Yace zasu ƙaddamar da wannan buki ne a Kasuwar Shanu ta Maliya da ke Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa. Kuma suna sa ran Fulani daga sassan Nijeriya da ma maqwbatakan kasashe za su hallara domin gudanar da wannan buki na al’ada.
A yau ake bikin Ranar Shan Fura ta Duniya