![](https://www.citynobs.com.ng/wp-content/uploads/2024/12/Tajudeen-Abbas-1-1024x570-1.jpeg)
Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya bayyana cewa, ba gaskiya ba ne rahotannin da ake yadawa cewa bukumomi a birnin yarayya na bin sa yana bin sa bashin kudaden mallakar filaye.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Musa Krishi, ya fitar a ranar Juma’a, Kakakin Majalisar ya ce yana da fili daya tak a birnin tarayya, wanda aka ba shi, kuma ya riga ya biya kudin filin tun watan Oktoban 2024, bayan sanarwar da FCTA ta yi a jaridu kan lamarin.
Ya ce kuskure ne FCTA ta sanya sunansa cikin jerin sunayen wadanda ba su biya kudaden filayensu ba, wanda hakan ya kai ga soke mallakar filayen.
Ya kuma shawarci FCTA da ta rika kula da irin wadannan al’amura kafin daukar mataki.
“An ja hankalin Kakakin Majalisar Wakilai, dangane da rahotannin da aka wallafa a kafafen watsa labarai, na cewa hukumar kula da birnin tarayya (FCTA) ta soke mallakar wasu filaye a birnin tarayya, ciki har da na Kakakin, saboda rashin biyan haraji.
Yace kakakin majalisar wakilai, yana da fili daya tak a birnin tarayya wanda aka ba shi, kuma tun watan Oktoban 2024 ya riga ya biya kudin bayan sanarwar da FCTA ta yi a jaridu.
Kakakin majalisar ya kuma gargadi kafafen watsa labarai da su tabbatar da sahihancin bayanansu kafin su wallafa irin wadannan labarai.
Abbas ya musanta raboton kwace masa fili