in

Ali Nuhu ya zama sabon jakadan Colgate a yankin Arewa

Kamfanin kula da lafiyar hakora, Colgate-Palmolive, ya bayyana fitaccen jarumin Kannywood da Nollywood, Ali Nuhu, a matsayin jakadan kayansu ga yankin arewacin Najeriya.

An kaddamar da jakadan ne a lokacin taron “Yanga with Your Smile” da aka gudanar kwanan nan a kasuwar Bata da ke Kano.

Manajan Tallace-tallace na Colgate a Arewa, Abdul Musa, a yayin da yake magana a wajen taron kaddamar da shirin, ya bayyana cewa zaɓen Ali Nuhu ya kawo asali ne sakamakon karɓuwarsa da shahararsa a Arewa, la’akari da rawar da yake takawa da tasirinsa a masana’antar fina-finan Najeriya.

Musa ya bayyana cewa Ali Nuhu shi ne ya fi dacewa wajen isar da saƙon muhimmancin kula da lafiyar hakora da kuma fa’idar amfani da kayan Colgate ta hanyar da ta dace da al’ummar yankin.

Ya bayyana cewa, “Muna matuƙar farin ciki da zaɓen Ali Nuhu a matsayin fuskar kayayyakinmu, musamman ga yankin Arewa. Shi mutum ne da jama’a suka saba da shi kuma suke girmamawa. Muna da tabbacin cewa tasirinsa zai taimaka wajen wayar da kan mutane kan kula da lafiyar hakora.

“Kamfaninmu ya himmatu wajen taimaka wa ’yan Najeriya su samu kwarin gwiwa da murmushi mai kyau.”

Ali Nuhu ya bayyana farin ciki da alfahari da haɗin gwiwarsa da Colgate a matsayin jakadan kayansu.

Ali Nuhu ya zama sabon jakadan Colgate a yankin Arewa

Silenced by fear, shame, stigma: Inside story of GBV victims

ACF ta taya Tanko Yakasai murnar cikar shekaru 99