Fitaccen mawaƙin Hausa a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, El-mu’az Muhammad Birniwa ya rasu.
Ya rasu ne a daren jiya Laraba Kuma za ayi janaizarsa kamar yadda addinin musulunci a safiyar yau,Alhamis.
El-mu’az ɗan asalin ƙaramar hukumar Birniwa ne ta jihar Jigawa, an haife shi a jihar Kaduna inda anan ya taso, ya gudanar da rayuwarsa.
Kuma kafin rasuwarsa yayi wakoki da dama, ciki harda na siyasa, ya kuma kasance mai shirya fina-fanai harma ya fito a wasu fina-fanan.
Tuni jaruman Kannywood suka fara wallafa sakon ta’aziyarsu ciki harda Ali nuhu da Falalu A Dorayi.
Allah ya yiwa fitaccen mawakin Hausa El-mu’az Birniwa Rasuwa