in

An kammala matatar Fatakwal da 90% – NNPCL

Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL) ya bayyana cewa sabon matatar mai ta Fatakwal ya kai sama da kashi 90 cikin ɗari na kammalawa.

Shugaban kamfanin, Mele Kyari ne ya bayyana hakan a ranar Litinin lokacin da shugabannin ƙwadago daga NLC da Ƙungiyar ƴan kasuwa ta TUC suka ziyarci matatar da ke jihar Ribas.

DAILY POST ruwaito cewa, bayan jinkiri mai tsawo da ya haɗa da gaza cimma wa’adin tayar da matatar sau bakwai, NNPC ta sanar da gyara matatar Fatakwal mai ɗaukar ganga 60,000 a kowace rana.

An fara aikin gyaran gaba ɗaya na matatar mai mai ɗaukar ganga 210,000 a kowace rana a shekarar 2021, bayan da gwamnatin tarayya ta samu kwangilar $1.5b domin gyara matatar, da ke cikin mummunan hali na shekaru da dama.

Da farko, NNPC ba ta bayyana adadin litan man fetur, dizel, man jirgin sama, da naphtha da matatar za ta samar ba, wanda ya saba wa mafi kyawun tsare-tsaren duniya.

Bayan shan suka, kamfanin ya ce matatar na tace lita miliyan 1.4 na man fetur a kowace rana, adadin da ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da tsarin duniya.

An kammala matatar Fatakwal da 90% – NNPCL

Ondo Guber: Ajayi files petition at tribunal over Aiyedatiwa’s victory

Governor Mohammed approves creation of Sayawa Chiefdom in Bauchi