in

An kashe ‘yan jarida 68 a cikin 2024 – Rohoton UNESCO

Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ta bayyana cewa a karo na biyu a jere, yankunan rikici sun zama masu hatsari ga ‘yan jarida da ma’aikatan yada labarai, inda a shekarar 2024 aka samu rasuwar akalla ‘yan jarida 68 yayin da suke aikinsu.

Sama da kashi 60 cikin 100 na wannan kashe-kashen sun faru a kasashen da ke cikin rikici – wannan shi ne mafi girman kaso cikin shekaru goma da suka wuce, a cewar sabbin bayanan UNESCO.

Shugabar UNESCO, Audrey Azoulay, ta bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis cewa, “Samun sahihan bayanai yana da muhimmanci a cikin yanayin rikici don taimaka wa al’ummomin da abin ya shafa da kuma wayar da kan duniya.”

Ta kara da cewa, “Ba abu ne mai karbuwa ba a ga ‘yan jarida suna biyan rayuwarsu saboda wannan aikin.”

“Nayi kira ga dukkan jihohi su tashi tsaye kuma su tabbatar da kariyar ma’aikatan yada labarai, bisa ga dokokin kasa da kasa,” ta kara da cewa.

Rahoton ya nuna cewa an kashe ‘yan jarida 42 a yankunan rikici a wannan shekara, ciki harda 18 a Palestine, wadda ta samu mafi yawan asarar rai.

Sauran kasashen kamar Ukraine, Colombia, Iraq, Lebanon, Myanmar, da Sudan suma sun sha wahala daga mummunan asarar rayuka, wanda ke nuna karuwar hadarin da ke akwai a yankunan da rikici da rashin tsaro ke ta’azzara.

An kashe ‘yan jarida 68 a cikin 2024 – Rohoton UNESCO

NNL: Gombe United sign 31 new players

Transfer: Lookman refuses to discuss Premier League return