Kyaftin din Kano Pillars, Rabiu Ali, na cikin yan wasa 18 da aka gayyata tare da Musa Zayyad na Elkanemi Warriors, da kuma Sikiru Alimi na Remo Stars domin bugawa tawagar Super Eagles wasa.
Babban mai horar da Super Eagles Augustine Eguavoen, ya kira yan wasa 18 domin bugawa tawagar wasan share fagen shiga gasar cin kofin nahiyar afrika ta yan wasan cikin gida da Kasar Ghana.
Gasar CHAN ta yan wasan da suke fafata wasa a nahiyar Afrika, za ta gudana a Fabrairun shekara mai kamawa a kasashen Kenya, Uganda, da kuma Tanzania.
Wasan farko na share fage dai tsakanin Najeriya da Ghana zai gudana a birnin Accra a ranar Lahadi 22 ga Disambar da muke ciki a kasar ta Ghana.
Jumullar yan wasa 18 da aka gayyata don buga wasan sun hadar da masu tsaran raga biyu
Henry Ozoemena (Enyimba FC); Kayode Bankole (Remo Stars).
Yan wasan baya kuwa: Ismail Sadiq (Remo Stars); Waliu Ojetoye (Ikorodu City); Imo Obot (Enyimba FC); Junior Nduka (Remo Stars); Victor Collins (Nasarawa United);
Ifeanyi Onyebuchi (Rangers International); Steven Manyo (Rivers United)
Yan wasan tsakiya kuwa akwai: Jide Fatokun (Remo Stars); Rabiu Ali (Kano Pillars); Saviour Isaac (Rangers International); Musa Zayyad (El-Kanemi Warriors)
Yan wasa masu cin kwallo kuwa akwai : Anas Yusuf (Nasarawa United); Adamu Abubakar (Plateau United) Sikiru Alimi (Remo Stars); Emmanuel Ogboloe (Kwara United); Papa Daniel Mustapha (Niger Tornadoes.
An kira kyaftin din Kano pillars bugawa Super Eagles wasa da Ghana