in

An kubutar da yara hudu daga hannun masu garkuwa a Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya tabbatar da sakin wasu yara hudu da aka yi garkuwa da su a garin Keke Millennium da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

DAILY POST ta tuna cewa an yi garkuwa da wasu yara uku ciki har da dan shekara biyu yayin da mahaifinsu ya je ya ziyarci matarsa da ke kula da tagwayensu a asibiti.

Masu garkuwa da mutanen sun fara neman Naira miliyan 300 a matsayin kudin fansa, amma daga baya sun mayar da kudin zuwa Naira miliyan 25. Sai dai Gwamna Uba Sani ya wallafa a shafin sa na Facebook yana tabbatar da sakin su.

“Mun sake yin wani abin azo a gani a kokarinmu na samar da zaman lafiya a jihar Kaduna. An sako yara 4 da aka yi garkuwa da su a garin Millennium da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna. Mal. Nuhu Ribadu, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya mika munsu ni kuma na hada yaran da iyayensu.”

Gwamna Uba Sani ya kara da cewa “Sakin yaran na daya daga cikin muhimman sakamakon yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar tattaunawa ta zaman lafiya da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa tare da hadin gwiwar ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro ta kasa.”

An kubutar da yara hudu daga hannun masu garkuwa a Kaduna

An kubutar da yara hudu daga hannun masu garkuwa a Abuja

Don’t milk Nigeria to death – Obi of Onitsha tells politicians