in

An saki Yahaya Bello daga gidan gyaran hali

Kotu ta saki tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, daga gidan gyaran hali na Kuje bayan cika sharuddan beli.

Kakakin hukumar gyaran hali ta kasa reshen Abuja, Adamu Duza, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a yammacin Juma’a.

Duza ya ce, “An sako Yahaya Bello bayan ya cika sharuddan belin. An sako shi a wannan yammacin (Juma’a).”

An bayar da belin sa a ranar Alhamis ta hannun mai Shari’a MaryAnne Anenih a kan kudi Naira miliyan 500.

Sharuddan sun hada da bayar da mutum uku da za su tsaya masa, kowannensu yana da kadarori a yankunan Maitama, Guzape, ko Asokoro a Abuja.

Kotun ta kuma umarci Bello da ya mika fasfo dinsa tare da haramta masa fita daga Najeriya ba tare da izini ba.

Tsohon gwamnan tare da Shuaibu Oricha da Abdulsalam Hudu suna fuskantar tuhume-tuhume guda 16 da suka hada da hadin baki, karya, cin amana, da mallakar kadarori ba bisa ka’ida ba, wanda Hukumar EFCC ta shigar.

Dukkansu uku sun musanta zarge-zargen.

Mai Shari’a Anenih ta ki amincewa da belin farko da Bello ya nema, amma ta bayar da beli ga wadanda ake tuhumar tare da shi.

Yayin da ta amince da sabuwar bukatar belinsa a ranar Alhamis, wanda ya kai ga sakin sa.

An saki Yahaya Bello daga gidan gyaran hali

An nada Halimai na riko 32 a Adamawa

Gov Nwifuru charges newly promoted military personnel to be patriotic