Gwamnatin jihar Kano ta ce ba ta tsoma baki a ayyukan hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jiha.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce zaici gaba da baiwa hukumar goyon baya dan yaki da cin hanci tsakanin jami’an gwamnati da duk wadanda suka ci kudin jama’a.
Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne a fadar gwamnatin kano a lokacin taron ranar yaki da cin hanci da rashawa da aka gudanar ranar Talata.
Majalisar dinkin Duniya ce ta ware duk ranar 12 ga watan Disamba don wayar da kan jama’a mahimmacin yaki da cin hanci da rashawa.
Amma Kano ba ta yi nata bikin bane saboda gwamna ba ya gari a ranar ranar ta 12 ga watan Disamba.
Gwamna ya nemi hukumar ta yaki da rashawa da karbar korafe korafe taci gaba da aikinta yadda ta sabayi ba tare da tsoro ba.
Ya kuma yaba da irin shugabancin da Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ke yi a jihar na yakar rashin gaskiya ba sani ba sabo.
Ba ruwanmu da aikin hukumar yaki da rashawa ta Kano – Gwamna Abba