in

Babu sansanin sojin wata kasa a Najeriya – Janar Christopher Musa

Shugaban hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa, ya musanta rahotannin da ke cewa an baiwa Faransa izinin kafa sansanin soji a Najeriya.

Janar Musa ya kalubalanci zargin da ke cewa ziyarar shugaban kasa Bola Tinubu zuwa Faransa, inda aka sanya hannu kan yarjejeniyoyi da dama, ta hada da baiwa kasashen waje damar kafa sansanin soji a Najeriya.

Ya yi wannan karin bayani ne a ranar Juma’a lokacin da ake gabatar da sabon tambarin Sojojin Najeriya na 2025 a hedkwatar tsaron kasa da ke Abuja.

A cewarsa, ba za a baiwa kowacce kasar waje damar kafa sansanin soji a Najeriya ba, ko a Arewa, ko a Kudu, ko a ko’ina.

“Babu wannan magana, Shugaban kasa ya san tasirin hakan, Yana kuma sane da cewa dole ne ya kare Najeriya, kuma ba zai taɓa yarda da kowanne ƙasashen waje ba.

“Saboda haka, ina so in yi amfani da wannan dama don yin wannan karin bayani,” in ji shi.

Shugaban hafsoshin tsaron ya kuma sake tabbatar da jajircewar rundunonin sojojin Najeriya wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Najeriya, Afirka, da duniya baki daya.

Babu sansanin sojin wata kasa a Najeriya – Janar Christopher Musa

Court jails 12 illegal scrap metal collectors in Delta

EFCC arrests 24 suspected internet fraudsters