Dangin Maryam Nasir Ado Bayero, diyar tubabben Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero, sun bayyana dalilin da ya sa aka dauke daurin aurenta da Jibrin Barau Jibrin, dan gidan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau daga Kano zuwa Abuja kamar yadda aka tsara tun da fari.
A wata sanarwa da Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Dan Agundi, ya fitar a ranar Litinin, bangaren amaryar sun yi watsi da rade-radin da ke alakanta matakin canja wajen daurin auren da tattaburzar da ake yi kan batun dokar gyaran haraji.
DAILY POST Hausa ta rawaito cewa a yan kwanakin nan Sanata Barau ya sha suka game da goyon bayan dokar gyaran harajin da shugaba Tinubu ya bijiro da ita, wadda shugabannin Arewa ke adawa da ita bisa zargin zata nakasta tattalin arzikin yankin.
Dan Agundi, wanda shi ne shugaban kwamitin shirya bikin a bangaren amaryar, ya bayyana cewa iyayen amarya ne suka yanke shawarar sauya wurin daurin auren ba bangaren ango ba.
“Shawarar sauya wurin daurin aure daga Kano zuwa Abuja ta fito ne daga Dangin amarya kawai, ba tare da sa bakin dangin angon ba. Bisa al’adarmu, alhakin zabar wurin daurin aure dama ya rataya ne a wuyan dangin amarya,” in ji shi.
Sanarwar ta bayyana cewa an yanke wannan shawara ne domin saukaka wa baki da zasu zo daga sassan Najeriya da kuma kasashen waje, ganin cewa Abuja tana da saukin zirga-zirga.
Dangane da siyasantar da batun, Dan Agundi ya gargadi jama’a da su kauce wa alakanta auren da wani lamari na siyasa, musamman dokar gyaran haraji.
“Aure ibada ne kuma bai kamata a danganta shi da siyasa ba. Muna kira ga masu yada jita-jita kan wannan batun da su daina nan take,” in ji sanarwar.
Babu siyasa a mayar da daurin auren dan gidan Barau zuwa Abuja – Dangin Amarya