in

Ban ce na goyi bayan kudirin gyaran dokar haraji 100% ba – Hon. Kofa

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru/Bebeji, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa ba ya goyon bayan kudirin gyaran haraji 100%.

Hon. Kofa ya bayyana haka ne ta cikin wata sanarwa da ya sa wa hannu, aka aika ga manema labarai a Kano.

Ya bayyana cewa babu wurin da ko sau daya, ya bayyana goyon baya ga duka abinda kudirin harajin ya kunsa.

“Abin da nace, akwai batutuwa da dama wadanda za su zama alheri ga Arewa da Nigeria.”

“Kuma mu yan Majalisa na yankin Arewa mu yi amfani da rinjayen da mu ke da shi a majalisa, mu tsaya daram mu goyi bayan duk wasu ƙudirorin da za su amfani Arewa ta fannonin bunƙasa tattalin arzikin yankin, waɗanda ke cikin ƙudirorin.”

“Mu kuma cire waɗanda za su cutar da mu ko mu gyarata a yadda ba za ta cutar da mu ba.”

“Kuma mu yi amfani da wannan damar dokar da aka kawo mu bijiro da wasu sabbi da muka tabbatar za su amfani Arewa, domin a shigar da su a cikin kundin ƙudirorin. A yayin haka kuma, mu tabbatar da yi wa sauran jihohi da yankunan Nigeria adalci a tsarin dokar. Amma ra’ayin wasu shi ne a yi watsi da dokar gaba ɗaya.”

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya kara da cewa ba zai taba goyon bayan wani abu da zai cutar da mazabarsa ko jihar Kano ko Arewa ba.

Ya ba jama’ar da ya ke wakilta, da sauran jagororin Arewa hakuri a kan abinda ya kira da rashin fahimtarsa.

Ban ce na goyi bayan kudirin gyaran dokar haraji 100% ba – Hon. Kofa

Man bags 18-month jail term for using paper to purchase motorcycle

Resemblance with Hilda Dokubo gave me my first Nollywood break — Nonso Diobi